|
Babu wata alaka tsakanin Hausa da Fulani sai ta zama wuri daya. Babu wata kabila Hausa-Fulani. Wannan sunan, Hausa-Fulani, yan jaridun kudancin Najeriya ne su ka kirkire shi. Ba za ka taba jin wani ya ce shi "Hausa-Fulani" ne ba. Ko Bahaushe ne kai, ko Bafillace -- ba bu tsaka-tsaki. Idan mahaifinka Bahaushe ne, ko kai Bahaushe ne. Idan Bafillace ne, to kai Pulaar ne.
Da yawa Fulanin yanzu sun manta da yaren su, ba don komai ba saboda iyaye da kakanni ba su koya mu su ba. Shi ya sa mutum zai yi tinkahon zama Bafilace, amma ko "zo in kashe ka" ba sani ba da Fillanci. Kamar ni. Na hada ruwan Fulani biyu -- Toranke (asali daga Bodinga ta hanyar kakana), Sullube (asali gidan Dabo, Kano, ta hanyar kakata). Amma ban iya Fullanci ba ko kadan -- kuma ina daga cikin mashawartan FULDAN, kungiyar mu ta Fulanin Najeriya. Rashin iya yaren asalinka ba sabon abu bane. Mu na da Larabawa da yawa a Arewacin Najeriya (Yemeni, Lebanese, Sudanese, North African), amma ba su iya Larabci ba -- amma kuma suna da hankilon cewa su Larabawa ne. Saboda haka AKIDAR da ka sakawa kanka ce ta ke tasiri, ba iya ko rashin iya yarenka ba. Kada ka manta Sarautar Daura a hannun HAUSAWA ta ke, ba Fulani ba. Ga wani karin bayani na makala game da Bayajida -- wanda ni a wajena kawai wani dan 419 ne, ko kuma kirkirar wani dan 419 a fadar Daurama domin a boye wani abu. |